Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-24 19:29:54    
Masu aikin sa-kai na birni na gasar wasannin Olympics ta Beijing suna tafiyar da ayyukansu ba ji ba gani

cri

Ko kuna sane da cewa, tun daga watan da muke ciki, tashohin masu aikin sa-kai sama da 500 a gundumomin Beijing guda 18 sun fara tafiyar da ayyukansu na bayar da hidima ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 wadda za'a yi nan ba da jimawa ba. Dubun-dubatar masu aikin sa-kai na birni na gasar wasannin Olympics ta Beijing sun soma ayyukansu daya bayan daya, domin bayar da hidimomi daga dukkan fannoni ga manema labaru, da 'yan kallo, da masu yawon shakatawa, da jama'a na gida da na waje, ciki har da ba su bayanai dangane da wuraren yawon shakatawa na Beijing, da dakuna da filayen gasar wasannin Olympics ta Beijing, da hasashen yanayi, da labarin kasa, da al'adun gargajiya na Beijing, da zaman rayuwa, da cin abinci, da sayen kayan sutura a birnin Beijing, tare kuma da zama mai fassara gare su, da ba su taimako cikin gaggawa. "Sannu! Don Allah ka gaya mini ta yaya ne nike zuwa tashar jirgin kasa? To, kana iya daukar motar safa mai lamba? "

He Xin, wani dalibi mai aikin sa-kai daga makarantar sana'a ta Huijia, wanda ke sanye da rigar aikin sa-kai mai launin shudi, ya fara aikinsa na nunawa masu yawon shakatawa hanyoyi tun daga ranar 1 ga watan Yuli. A matsayin wani mai aikin sa-kai na gasar wasannin Olympics ta Beijing a gundumar Changping ta birnin Beijing, babban nauyin dake bisa wuyan He Xin shi ne, nuna hanyoyi zuwa dakuna da filayen gasar tseren mutum daya kakkarfa cikin wasanni uku, wato wasan Triathlon dake kunshe da wasan iyo, da gudun fanfalake da kuma na tseren keke kan hanyar mota, da muhimman hanyoyi zuwa wuraren yawon shakatawa na Changping. Domin zama wani kyakkyawan mai aikin sa-kai, He Xin ya riga ya karbi horon musamman har na tsawon watanni biyu. Ya ce:

"Ina aiki ne a tashoshin bayar da hidima guda biyu dake manyan mahadar motar-safa biyu a gundumar Changping, wadanda ke kunshe da masu aikin sa-kai da dama. Mun karbi horon musamman har na tsawon watanni biyu, domin karo ilimi dangane da wuraren yawon shakatawa, da hanyoyi zuwa dakuna da filayen gasannin Olympics a gundumar Changping, da yadda za mu yi domin yin ceto cikin gaggawa, da dai sauran makamantansu."

Aikin nuna hanyoyi ga mutane, wani babban aiki ne ga masu aikin sa-kai na birni. A gundumar Xuanwu ta birnin Beijing, akwai wata karamar kungiya wadda ke kunshe da mata zalla, babban aikinsu shi ne nuna hanyoyi ga mutane. Madam Zhao tana daya daga cikinsu, wadda ke daukar nauyin nunawa mutane hanyoyi zuwa sanannun wuraren yawon shakatawa na Beijing. Ta gayawa wakilinmu cewa, kamata ya yi ta kara sanin wuraren yawon shakatawa, da dakuna da filaye na gasar wasannin Olympics, da zirga-zirgar motar safa dake kewaye da tashoshin bada hidima, kazalika kuma, ya kamata ta koyi harshen Turanci domin nuna hanyoyi ga baki 'yan kasashen waje. Madam Zhao ta ce: "Kullum mu kan gamu da wasu baki 'yan kasashen waje wadanda suka tambaye mu hanyoyi zuwa wurare kaza da kaza, dukkan membobin kungiyarmu muna ganin cewar, tilas ne mu koyi harshen Turanci. Sabili da haka ne, muka gayyaci wani malami domin koyar mana da harshen Turanci. Mun dora muhimmanci sosai kan koyon wasu muhimman kalmomi da jumloli cikin Turanci, kamar su gidajen cin abinci, da tashohin mota dake kewaye da wannan wuri, da wasu sanannun wuraren da baki 'yan kasashen waje suke so su je ziyara, ciki har da dakin gudanar da gasannin ninkaya na wasannin Olympics wato 'Water Cube', da filin wasa na 'Bird's Nest' mai siffar shekar tsuntsaye, da gidan sarakuna, da babbar ganuwar Sin wato Great Wall da dai sauransu."

Ko shakka babu, a duk tsawon lokacin gasar wasannin Olympics ta Beijing, wannan karamar kungiyar dake kunshe da mata zalla, wadanda ke sanye da tufufin aikin sa-kai iri daya, za ta bayar da kyakkyawar hidima ga baki 'yan kasashen ketare cikin harshen Turanci.

"Bayan da muka samu horo na musamman a kan harshen Turanci, yanzu, ba ma kawai muna iya fahimtar abubuwan da suka fadi ba, hatta ma muna iya yin amfani da cikakkun jumloli cikin Turanci domin amsa tambayoyinsu. Yayin da suke amsa mana cewa 'thank you very much', mu ma muna farin-ciki kamar su. Yayin da mu Sinawa muke bayar da taimako ga baki 'yan kasashen waje, muna jin dadi sosai."

A cikin tashoshin masu aikin sa-kai da dama a nan Beijing, nakasassu masu aikin sa-kai sun fi jawo hankulan mutane. Akwai wata nakasasshiya mai suna Gao Yuhong, wadda ba ta iya tafiya da kafa a sakamakon mummunar cutar shan-inna, ita ce shugabar kungiyar nuna hanyoyi ta gundumar Haidian ta birnin Beijing. A kowane karshen mako, ta kan je kofar Fadar Bazara ta arewa, a wani yunkurin nuna hanyoyi ga masu yawon shakatawa na gida da na ketare.

"Na kamu da cutar shan-inna tun lokacin da nike karama, na samu taimako daga bangarori daban-daban na dukkan zamantakewar al'umma. Domin bayar da gudummowata ga zamantakewar al'umma, na kafa wannan karamar kungiya bisa taimakon da aka ba ni a shekaru biyu da suka gabata."

1 2 3