
Ra'ayoyin bainal jama'a sun lura da cewa, ko da yake Amurka ta nuna sassauci wajen matsayin da ta dauka kan kasar Iran, amma babban matsayinta bai sauya ba. Cikin shekaru 2 da suka wuce, gwamnatin Bush ta nuna tsattauran ra'ayi kan matsalar nukiliya ta Iran, ta nemi Iran a kan dole ne ta tsayar da shirin tace sinadarin Uranium, sai da haka ne kawai za ta iya yin shawarwari da ita a hukunce. Sabo da haka ana iya cewa, ba mai yiwuwa sosai ba gefunan 2 za su iya samun babban sakamako ta hanyar yin wannan shawarwari. (Umaru) 1 2 3
|