
Canjin manufar da Amurka ke yi kan kasar Iran ba ma kawai ya shafi saduwar da ake yi tsakanin manyan shugabannin kasashen 2 ba, cikin 'yan makonnin da suka wuce, fadar gwamnatin Amurka wato white house kuma ta kaddamar da wani shirin ba da lambobin yabo masu gatanci ga kasar Iran, ciki har da yin alkawari cewa za a daidaita matsalar nukiliya ta Iran ta hanyar rishin yin amfani da karfin makamai, da yin tattaunawa sosai a tsakaninta da Iran kan matsalar tsaron kasar, da nuna goyon bayanta ga kasar Iran don ta taka muhimiyyar rawa cikin harkokin kasashen duniya. Sa'an nan kuma Amurka ta nuna goyon bayanta ga kungiyar EU da ta yi shawarwari bisa mataki na farko a tsakaninta da Iran, kuma ta gaya wa Isra'ila a fili cewa, kada ta dauki matakin soja kan kasar Iran daga gefenta kawai.
Mahukuntan Amurka sun jaddada cewa, muhimmin dalilin da ya sa Amurka ta canja manufar da ta dauka kan kasar Iran shi ne, ta riga ta gani cewa, an riga an samu sakamako wajen takunkumin da kasashen duniya ke sa wa kasar Iran wajen tattalin arziki, kasar Iran ita ma ta samu sabbin sauye-sauye wajen manufar da ta dauka kan kasar Amurka, kuma ta nuna sassauci kan wasu matsaloli. Ban da wannan kuma fadar gwamnatin Amurka ita ma tana ganin cewa, wajibi ne ta yi gyare-gyare ga manufofin da ta dauka a da, kuma ta nanata magana kan muhimmancin kokarin da ta yi a fannin harkokin waje.
1 2 3
|