Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-18 13:13:49    
Amurka ta nuna sassauci wajen matsayin da ta dauka kan matsalar nukiliya ta Iran

cri

A ran 16 ga wata, gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, Mr. Williams Burns, mataimakin sakataren harkokin waje mai kula da harkokin siyasa na kasar zai halarci shawarwarin da za a yi a ran 19 ga wata a birnin Geneva a tsakanin Mr. Solana, babban wakili mai kula da manufofin harkokin waje da tsaron EU wato kungiyar tarayyar kasashen Turai da Mr. Saeed Jalili, wakili na farko na kasar Iran a gun shawarwarin nukiliya. Wannan ya bayyana cewa, manufar da Amurka ta dauka kan kasar Iran ta samu sassautuwa.

Bayan da aka katse huldar diplomasiya a shekarar 1980 a tsakanin Amurka da Iran, har ila yau ba su tabbatar da mayar da dangantakar da ke tsakaninsu yadda ya kamata ba tukuna. A shekarar 2002 shugaba Bush na Amurka ya mai da kasar Iran a matsayin "muhimmiyar kasa mai barkata mugunta", kuma ya jaddada cewa, kafin kasar Iran ta tsayar da shirinta na tace sinadarin Uranium, Amurka ba za ta yin shawarwari kai tsaye a tsakaninta da ita ba, sa'an nan kuma ya bayyana cewa, mai yiwuwa ne Amurka za ta yin amfani da karfin makamai ga kasar Iran. Amma yanzu ba zato ba tsammani Amurka ta sanar da cewa, za ta aike da babban mutum na 3 na majalisar harkokin kasashen waje ta kasar don yin shawarwari da kasar Iran, ban da wannan kuma bisa goyon bayan da madam Condoleezza Rice ta bayar, Mr. Burns ya riga ya ja gaba wajen tsara shirin kafa wata tashar yin cudanya ta kasar Amurka da ke kasar Iran a fannin harkokin waje.


1 2 3