Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:30:19    
Titin Wangfujing na jiran matafiya na gida da na waje

cri

Ire-iren irin wadannan abubuwan da ake sayarwa a shagun sayar da kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman da ke cikin babban ginin sayar da abubuwan fasaha na Wangfujing sun fi yawa. Madam Zhang ta yi mana karin bayani da cewa,

'A gun gasannin wasannin Olympic da aka yi a da, a kan bude wani babban shagon sayar da kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman a cibiyar birni. Shagonmu ya fi girma a cikin dukkan shagunan kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman a yanzu. Ire-iren kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman da ake sayarwa a nan sun fi yawa, ta haka za mu iya nuna irin wadannan abubuwa daga dukkan fannoni. Kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman sun hada da manyan ire-ire 15 da kuma kayayyaki iri-iri fiye da dubu 7, ciki har da hankici na kudin Sin yuan 5 da kuma sandar zinariya na yuan miliyan 1 da dubu 80, wadda ta fi tsada. In kun kawo wa shagunanmu ziyara, to, za ku iya kallon dukkan kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman.'

Kazalika kuma, akwai shahararrun dakunan cin abinci da kantunan sayar da abinci masu nuna halayen musamman a titin Wangfujing mai dogon tarihi. In kuna son ku sayi littattafai, akwai kantunan sayar da littattafai a titin, inda ake sayar da littattafai iri daban daban. Mun yi imani da cewa, a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, in kun sami damar kawo wa Beijing ziyara, to, tabbas ne za ku yi yawo a titi Wangfujing.


1 2 3 4