Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:30:19    
Titin Wangfujing na jiran matafiya na gida da na waje

cri

Kantin Suifuxiang, wani kanti ne da ya yi shekaru fiye da dari daya yana sayar da siliki da zane. Reshen Suifuxiang a titin Wangfujing yana dogara da sayar da siliki, haka kuma, yana sayar da sauran ire-iren zane masu inganci da kuma tufafi irin gargajiya na na al'ummar Sin, kamar Qipao, wato wata irin rigar gargajiya da matan kabilar Man ta kasar Sin suka taba sanyawa. Silikin da ake sayarwa a kantin Ruifuxiang kayayyaki ne da mashahurran masana'antun samar da siliki na biranen Shanghai da Hangzhou da Suzhou suke samarwa, sun shahara ne sosai saboda ingancinsu mai kyau. Matan jakadun kasashen waje masu yawa a kasar Sin da kuma matan shugabannin kasashen waje da yawa da suka kawo wa kasar Sin ziyara su kan sayi siliki da 'yan kwali da kuma tufafin da aka yi da siliki a kantin Ruifuxiang. Domin bai wa masu saye-saye sauki, akwai madinka a reshen Ruiguxiang a titin Wangfujing. In ka sayi yadi a nan, to, nan da nan madinka za su auna ka domin dinka maka tufafi.

A reshen Ruifuxiang a titin Wangfujing, mun gamu da Jodie Roussell, wata budurwa da ta zo daga kasar Amurka. Kawarta da ita sun sayi siliki daga Hangzhou, sun yi shirin yin tufafi irin na Qipao da tufafi.

'Titin Wangfujing ya yi suna sosai. A ko wane karo da na kawo Beijing ziyara, na kan yi saye-saye a titin. Abokaina da ni mun taba yin tufafi a wannan kanti. Ingancin silikin da ake sayarwa a nan yana da kyau kwarai, haka kuma ana sayar da dimbin abubuwan siliki da aka yi da hannu, kuma sun zo daga Hangzhou. Shi ya sa a ko wane karo da na kawo wa kasar Sin ziyara, na zo wannan kanti saboda ingancin siliki mai kyau da siliki mai rahusa da kuma hidima mai kyau. In kun zo titin Wangfujing, to, tabbas ne za ku shiga kantin Ruifuxiang.'


1 2 3 4