Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:30:19    
Titin Wangfujing na jiran matafiya na gida da na waje

cri

In kun yi saye-saye a titin Wangfujing, kada ku manta da shagunan sayar da kayayyakin fasaha irin na gargajiya na kasar Sin. Babban ginin sayar da kayayyakin fasaha na Wangfujing wani zabi ne mai kyau a gare ku. Zhang Mingyue, shugaban sashen kula da harkokin sayarwa na wannan babban gini ta yi mana karin bayani da cewa,

'Babban ginin sayar da kayayyakin fasaha na Wangfujing kanti ne na sayar da kayayyakin fasaha da ya fi shahara a kasar Sin. Ana sayar da dukkan ire-iren kayayyakin fasaha na kasar Sin, haka kuma, ana sayar da kayayyakin fasaha da ke nuna halin musamman na birane da larduna na kasar Sin. Alal misali, yadin da aka rina irin na Guizhou da kayayyakin fenti na Yangzhou, da abubuwa masu yawan dinki na Hangzhou, da abubuwan fasaha da aka yi da hannu a kudu da kogin Yangtse, da takardun da aka yanke da almakashi na Hebei da mutum-mutumin tabo na Tianjin. Yawan ire-iren kayayyakin fasaha da ake sayarwa a nan ya kai dubu gomai.'

Madam Zhang ta ci gaba da cewa, ban da fitattun kayayyakin fasaha kamar abubuwan da aka yi da hauren giwa da lu'ulu'u da dai sauransu, akwai takardun da aka yanke da almakashi da fifilo da mutum-mutumin tabo da sauran abubuwan fasaha da aka yi da hannu, su ma suna nuna halin musamman na kasar Sin, amma suna da rahusa sosai, sun cancanci zama abubuwan kyauta da aka bai wa abokai da dangogi.

Bayan da muka ziyarci shahararrun kantuna masu tsawon daruruwan shekaru a titin Wangfujing, bari mu ci gaba da ziyararmu a titin Wangfujing.

A babban kantin Beijing APM, mun gamu da Mark da masoyiyyarsa Claire da suka kawo wa kasar Sin ziyara daga kasar Ireland. Yaya ra'ayoyinsu kan wadannan manyan kantuna a titin Wangfujing.

'Wannan babban kanti ya yi kama da na kasar mu Ireland, inda ake sayar da kayayyaki iri daya.'

'Amma a ganina, wannan kanti na Beijing APM yana da girma sosai, zai kai wani karamin gari. Kana iya samun kome da kome. Sa'an nan kuma, ana nuna fina-finai da Turanci a gidan sinima a nan. Masu yawon shakataka daga kasashen waje za su ji sauki. Ban da wannan kuma, in kun ji gajiya a sakamakon tafiye-tafiye a Beijing, to, za ku iya sakin jiki a nan.'

Saboda kusantowar gasar wasannin Olympic ta Beijing, ana kara samun yanayin wasannin Olympic a titin Wangfujing. A wannan titi, kusan ko wane babban kanti yana da shaguna daya ko kuma biyu na sayar da kayayyakin gasar wasannin Olympic bisa iznin musamman.


1 2 3 4