
Wani jami'in samar da hidimar yanayin sararin samaniya na kasar Sin mai suna Chen Zhenlin ya bayyana cewa, a lokacin da muke shirya wasannin Olimpic, kwararrun da suka kware sosai wajen yanayi kuma suka zo daga kasar Amurka da Australiya da Canada da Japan da Hongkong za su sauko nan birnin Beijing don hadin kai da kwararrun kasar Sin wajen bayar da rahoton yanayi. Mr Chen ya bayyana cewa, kowanenmu ya mai da hankali ga yanayin sararin samaniya a lokacin yin wasannin Olimpic, irin hadin kanmu zai ba da taimako sosai ga kara daga ingancin fasaharmu da kuma ba da misali ga duk duniya wajen hadin kai kan yanayi.

Mr Qiao Lin ya bayyana cewa, a wajen fannin sa ido da tsarin ba da rahoto da gine-gine da horar da ma'aikata masu bayar da rahoto, mun riga mun shiga cikin halin yin kome da kome. A lokacin da muke yin gasanin wasannin Olimpic, za mu samar da hidimar yanayi ga dukkan dakuna da filaye na yin wasannin Olimpic ba tare da katsewa ba.(Halima) 1 2 3
|