Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:02:52    
Sassan yanayin sararin samaniya na kasar Sin za su samar da hidima mai inganci ga wasannin Olimpic na Beijing wajen yanayin sararin samaniya

cri

Dayake yanayin sararin samaniya zai sami sauyawa da ba za a iya tabbatar da shi ba, shi ya sa yaya za a ba da rahoton yanayi yadda ya kamata ya zama batu mai wuyar warwarewa ga duk duniya, musamman ma bisa sharadin kara dumin yanayin sararin samaniya a duk duniya, yanayi maras kyau sosai yana kan faruwa, shi ya sa ake kan gabatar da kalubale ga aikin bayar da rahoto kan yanayi. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta kara karfin sa ido kan bala'in da ya faru bisa sakamakon yanayin sararin samaniya, kuma ta zuba jari da yawa don kara kyautata da daga matsayin tsarin ko ta kwana kan yanayin sararin samaniya. A ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 2008, kasar Sin ta harba wani tauraron dan adam na yanayin sararin samaniya mai lamba Fengyun-3 wanda ita kanta ta yi bincike da kera shi. Tauraron zai ba da taimako ga bayar da rahoton yanayin sararin samaniya dangane da kwanaki goma zuwa 15, wannan tauraron zai kara karfin kasar Sin sosai wajen binciken yanayin sararin samaniya. Yanzu tauraron yana shiga matakin yin gwaje-gwaje a kan hanyarsa, kuma ya riga ya bayar da taswirar gizagizai ta yanayin sararin samniya da kyau, ana sa ran soma aiki da shi kafin wasannin Olimpic.


1 2 3