Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-16 15:02:52    
Sassan yanayin sararin samaniya na kasar Sin za su samar da hidima mai inganci ga wasannin Olimpic na Beijing wajen yanayin sararin samaniya

cri

Sauye-sauyen yanayin sararin samaniya za su ba da tasiri mai muhimmanci sosai ga gudanar da gasannin wasannin Olimpic na Beijing lami lafiya da samun sakamakon da 'yan wasa za su yi yadda ya kamata. A ranar 15 ga wannan wata, a nan birnin Beijing, wani jami'in da abin ya shafa na sashen yanayin sararin samaniya ya bayyana cewa, sassan yanayin sararin samaniya na kasar Sin sun riga sun dauki matakai da yawa don kara karfi ga bayar da rahoton yanayin sararin samaniya da kuma samar da hidimar da ta dace dace wasannin Olimpic a daidai lokaci.

Samar da rahoton yanayin sararin samaniya yadda ya kamata a daidai lokaci na da ma'ana mai muhimmanci sosai ga gasannin wasannin Olimpic, musamman ma ga bikin bude wasannin Olimpic da za a shirya a daidai lokacin da aka shriya yadda ya kamata. A wani taron bayar da labarai da aka shirya a ranar 15 ga wannan wata a nan birnin Beijing, kwararren farko na bayar da rahoton yanayin sararin samaniya na cibiyar yanayin sararin samaniya ta hukumar yanayin sararin samaniya ta kasar Sin Mr Qiao Lin ya bayyana cewa, kafin ranar 8 ga watan Augustan da ya rage mako guda , za mu gabatar da rahoton yanayin sararin samaniya a lokacin da za a yi bikin bude wasannin Olimpic, ban da wannan kuma, za mu bayar da labarin ko ta kwana kan yanayin sararin samaniya maras kyau sosai da ba a yi tsammanin faruwa ba, alal misali, ana ruwan sama kamar da bakin kwarya da babbar guguwa da sauransu a daidai lokaci ko kafin wasu sa'o'I , don jawo hankulan sassan da abin ya shafa, ciki har da 'yan wasa da sassan da suke da nasaba da 'yan wasa, don su mai da hankulansu ga irin wannan yanayin sararin samaniya.


1 2 3