Mataimakin ministan tsare ruwa na kasar Sin Mr. Jiao Yong ya bayyana cewa, sassan da abin ya shafa na kasar Sin sun mai da hankula sosai kan ayyukan yaki da ambaliyar ruwa a wannan shekarar da muke ciki. A yayin da suke fama da girgizar kasa, sun dauki matakai a jere domin tinkarar bala'un ambaliyar ruwa da mai yiyuwa ne za su faru. Mr. Jiao ya ce,
'Na farko, sassan daban daban sun dudduba ayyukan tsare ruwa, hukumomin tsare ruwa na duk kasar Sin sun kebe kwararru dubu uku da dari biyu da tamanin domin dudduba ayyukan tsare ruwa. Na biyu, sun tabbatar da nauyin da ke bisa wuyansu, na uku, sun dauki matakai cikin gaggawa domin yaki da girgizar kasa da ambaliyar ruwa, na hudu, sun kawar da hadari daga ayyukan tsare ruwa da suka lalace sakamakon girgizar kasa.'
1 2 3
|