A ran 2 ga wata a birnin Beijing, wani jami'in ma'aikatar tsare ruwa ta kasar Sin ya bayyana cewa, a halin yanzu dai, kasar Sin tana kokari da take iya yi wajen yin gyare gyaren ayyukan tsare ruwa da suka lalace sakamakon girgizar kasa, da kawar da hadarin tafkin da ya samo asali daga girgizar kasa cikin gaggawa, domin tabbatar da daidaita matsalolin da yankunan girgizar kasa na lardin Sichuan su kan fuskanta a lokacin ambaliyar ruwa.
Tun daga ran 1 ga wata, yankunan girgizar kasa na lardin Sichuan sun shiga cikin muhimmin lokacin ambaliyar ruwa. Bisa hasashen yanayi da aka yi, an ce, a cikin shekarar da muke ciki, ruwan sama a babban wa'adin ambaliya ya fi yawa a tarihi. Bisa mummunan tasiri da aka samu daga babbar girgizar kasa, karfin ayyukan tsare ruwa na wadannan yankuna ya ragu wajen yaki da ambaliyar ruwa, haka kuma, har yanzu ba a kawar da hadarin tafkin da ya samo asali daga girgizar kasa sosai ba, wadannan sababbin halaye sun kara haddasa matsaloli ga ayyukan yaki da ambaliyar ruwa.
1 2 3
|