A ran 29 ga watan Maris na shekarar bana, an yi babban zabe a Zimbabwe bayan da ta samu mulki kai, jam'iyyar adawa wato jam'iyyar MDC ta samu rinjaye a cikin zaben, haka kuma, yawan kuri'un da dan takarar shugaban kasar na wannan jam'iyyar Morgan Tsvangirai ya samu ya fi 'dan takara na jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasa Robert Mugabe, amma bai wuce rabin kuri'un da aka kayyade ba, shi ya sa dole ne a kada kuri'u na zagaye na 2 a ran 27 ga watan Yuni. Amma kafin zabe na zagaye na 2, Mr. Tsvangirai ya janye daga zaben bisa dalilin barkewar tashe-tashen hankula da rashin daidaici a cikin zabe, kuma ya yi tsammani cewa, kada kuri'u na zagaye na biyu ya karya doka, ba zai amince da sakamakonsa ba.
Masu nazari sun nuna cewa, jam'iyyar MDC tana fuskantar hali mai tsanani, wato dole ne ta yarda da shiga cikin musanyar ra'ayi, idan ba ta yi haka ba, za ta yi laifin lalata yanayin yin shawarwari, ta yadda za ta rasa goyon baya da jama'ar Zimbabwe suka nuna masa. Amma ba ta shirya sosai ba kan batun kafa gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasa. Idan ta amince da kafa gwamnatin, dole ne ta yanke kudurin shiga cikin gwamnati ko majalisar dattijai ko majalisar wakilai. Idan ba ta yi la'akari sosai kan wadannan batutuwa ba, mai yiwuwa ne, jam'iyyar adawa za ta kama matsayin maras rinjaye a gun shawarwari na nan gaba. 1 2 3
|