A ran 2 ga wata, bi da bi ne, jam'iyyar ZANU-PF dake kan karagar mulkin kasar Zimbabwe da muhimmiyar jam'iyyar adawa wato jam'iyyar MDC sun mai da martani ga kudurin da taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Afrika wato kungiyar AU ya yi dangane da halin da ake ciki a kasar Zimbabwe. Jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasa ta yi maraba da wannan kuduri, amma jam'iyyar MDC ta ki karbar kudurin, kuma ta furta cewa, ba za ta kafa gwamnatin hadin gwiwar al'umma bisa sharadin da ke kasancewa yanzu ba, amma tana son ta yi musanyar ra'ayi tare da jam'iyyar ZANU-PF don daidaita kalubalen da kasar take fuskanta.
Batun Zimbabwe yana daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a gun taron koli na kungiyar AU da aka rufe ba da dadewa ba, taron ya zartas da kuduri a karshe, inda aka kalubalanci bangarorin da abin ya shafa da su yi musanyar ra'ayi. Kudurin ya ce, dole ne a hana lalacewar halin da ake ciki da kuma kafa wani muhalli mai kawo moriya ga dimokuradiyya da bunkasuwa na Zimbabwe. Bugu da kari, kudurin ya sa kaimi ga shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da shugaban jam'iyyar adawa Morgan Tsvangirai da su cika alkawarinsu na yin shawarwari. Dadin dadawa, kudurin ya nuna goyon baya ga ra'ayin bangarorin biyu wajen kafa gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar, kuma ya nuna goyon baya ga aikin sulhuntawa da tarayyar bunkasuwar kasashen kudancin Afrika ta yi.
1 2 3
|