Jam'iyyar ZANU-PF dake kan karagar mulkin kasar Zimbabwe ta yi maraba da kudurin da kungiyar AU ta yi, tana ganin cewa, wannan kuduri ya dace da ra'ayin shugaba Mugabe. A madadin gwamnatin kasar, ministan watsa labaru da harkokin yau da kullum na Zimbabwe Sikhanyiso Ndlovu ya ce, kudurin kungiyar AU ya nuna goyon baya sosai ga sanarwar da shugaba Mugabe ya yi wajen yin musanyar ra'ayi da kafa gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar. A ran 29 ga watan Yuni, Mr. Mugabe ya taba nuna a gun bikin ranstuwar kama aikin sabon shugaban kasar cewa, domin makomar dinkuwar kasa daya da hadin gwiwar alumma, ya kamata, jam'iyyu daban daban su rage sabane-sabane tsakaninsu da kara hadin gwiwa.
Bayan da shugaban muhimmiyar jam'iyyar adawa ta Zimbabwe wato jam'iyyar MDC Morgan Tsvangirai ya san wannan kuduri, ya ki karbar kudurin da kungiyar AU ta yi wajen kafa gwamnatin hadin gwiwar al'ummar kasar tare da shugaba Mugabe, a ganinsa, hakan ba zai ingiza daidaita rikicin kasar ba.
1 2 3
|