Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 15:26:24    
Hong Kong tana maraba da ku domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

She Jingyu, darektan sashen kula da dakunan dawaki na shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ya nuna mana dakin dawaki mai taurari 6 da aka yi amfani da injin sanyaya daki a awoyi 24, wannan zai tabbatar da lafiyar dawaki a lokacin gudanar da gasar wasannin Olympic. Mr. She ya ce,'Akwai wani wurin fitar da iska a cikin ko wane dakin dawaki, shi ya da zafi zai yi daidai a duk dakin dawaki. Za a canza iska da kuma kashe kwayoyi a ko wadanne awoyi 2 a nan.'

A kwanan baya, Sun Guiliang, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin 'yan sanda na Hong Kong ya yi farin ciki sosai, saboda sun sami cikakken goyon baya daga mazauna Hong Kong wajen gudanar da ayyukan tsaron kai. Ya ce,'Tabbas ne mazaunan wurin, musamman ma wadanda suke zama a Shatian za su gamu da matsala a fannin zirga-zirga. Mun tsara cikakken shiri domin yin wa mazauna Hong Kong bayani kan matsalolin da za su fuskanta. Bisa yanayin da muke ciki yanzu, mun yi imani da cewa, za mu sami goyon baya daga dukkan mazauna Hong Kong, musamman ma wadanda ke zama a Shatian.'

A maimakon gina sabon kauyen wasannin Olympic, Hong Kong ta yi kwaskwarima kan wani otel domin saukar da 'yan wasan da za su shiga shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing. Liang Aishi, shugabar kauyen wasannin Olympic na Hong Kong tana ganin cewa, wannan ba zai kawo illa ga Hong Kong da ta bai wa 'yan wasa na kasashe daban daban farin ciki ba. Ta ce,'Ko da yake otel din ba shi da girma, amma za mu iya samar da hidima daga dukkan fannoni. Mun kebe wani bene da ya zama cibiyar ba da hidima, ciki har da banki da gidan waya. Za mu samar wa 'yan wasa wani wurin jin dadi, kuma, a lokacin hutu, 'yan wasa za su iya kara saninsu kan Hong Kong.'

A madadin hukumar yankin musamman na Hong Kong, Tang Yingnian, shugaban sashen kula da harkokin hukumar Hong Kong kuma shugaban kwamitin Hong Kong na shirya shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing ya gayyaci 'yan kallo na duk duniya, ya kuma bayyana cewa, Hong Kong tana da aniyar gudanar da gasar sukuwar dawaki na babban mataki mai halin musamman. Mr. Tang ya ce,'Bisa babban tunaninsa na 'Kasa daya amma tsarin mulki 2', Mr. Deng Xiaoping ya taba bayyana cewa, za a ci gaba da gasar sukuwar dawaki da raye-raye bayan da Hong Kong ta koma karkashin shugabancin kasar Sin. Yin shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing zai kara sabon fanni a cikin bayanin Mr. Deng. Garinmu na Hong Kong, babban birni ne da ake yin zama cude-ni-in-cude-ka, shi ya sa muke ganin cewa, za mu iya ba da taimako wajen shirya gasar wasannin Olumpic na babban mataki kuma mai halin musamman.'(Tasallah)


1 2 3