Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 15:26:24    
Hong Kong tana maraba da ku domin shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Masu karatu, za a yi shirin sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a watan Agusta na wannan shekara a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. A yayin da ya rage sauran wata guda ko fiye kawai da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, ko Hong Kong ta share fage? Yau ma bari mu karanta bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana daga wannan yanki.

Dare ya yi duhu, an fara kunna fitilu a manyan gine-gine, yawan mutanen da ke kaiwa da kawowa a titin Miaojie ya soma karuwa. Kullum ana sayar da kayayyaki masu rahusa iri daban daban a titin. Mutane da yawa su kan ce, sun iya gano ruhun mazauna Hong Kong daga wannan titi, wato rashin jin tsoron jure wahala da kuma rika yin kokari ba tare da kasala ba. A gefunan titin, mazauna wurin sun fara rera tsohuwar waka da yaren Yue, wato yaren Guangzhou.

Mr. Guan mai shekaru 30 ko fiye da haihuwa yana tafiyar da wani dakin cin abinci mai tsawon shekaru 58 a titin Miaojie, wanda ke matsayin dan kallo ne da ke ganin sauye-sauyen Hong Kong. Mr. Guan ya gaya mana cewa, bayan wata guda ko fiye, dakin cin abincinsa zai sake zama dan kallo ga wani lamarin musamman, wato shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic da za a yi a Hong Kong. Ya ce,'Shirya shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic a Hong Kong ya kawo wa Hong Kong alheri. Har kullum mazauna Hong Kong suna fi kaunar kallon gasar tsunduma cikin ruwa da ta wasan lankwashe jiki, wadanda 'yan kasar Sin suka fi gwanance. Mazauna Hong Kong su kan yi ban tafi a yayin 'yan wasan Sin suka sami lambobin yabo.'


1 2 3