Kafin Hong Kong ya koma karkashin shugabancin kasar Sin a shekarar 1997, kasar Birtaniya ta dade tana yin mulkin mallaka a Hong Kong. Gasar sukuwar dawaki ita ce gasar gargajiya da mutanen Birtaniya suka dade suna himmatuwa a kai. Saboda tasirin mutanen Birtaniya, a shekarar 1846, an yi gasar sukuwar dawaki a karo na farko a Paomadi ta Hong Kong. Bayan shekaru 100 ko fiye, ya zuwa yanzu, Paomadi ta kan cika da mutane da yawa a lokacin gasa, wato ko wace ranar Laraba da ko wane karshen wata.
A lokacin zafi na shekarar 2005, kwamitin wasannin Olympic na duniya ya tsai da kudurin yin shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing a Hong Kong. Wen Siming, shugaban cibiyar gwaje-gwaje ta hadaddiyar kungiyar sukuwar dawaki ta Hong Kong ya gaya mana cewa, kullum Hong Kong tana bin matakai mafi tsaurara wajen yin binciken dawaki a cikin gasar sukuwar dawaki, shi ya sa babu tamtama shirin sukuwar dawaki ta gasar wasannin Olympic ba zai dame ta ba, inda za a yi bincike kan dawaki maras yawa. Mr, Wen ya ce,'Kullum mu kan yi bincike kan abubuwan misali fiye da dubu 18 a ko wace shekara. A gun gasar wasannin Olympic, ba za mu yi bincike kan abubuwan misali masu yawan haka ba, a ganina, watakila za mu yi dawaki 50 ko fiye kawai.'
Amma shirya wannan gasar motsa jiki mafi koli a tarihinta ya kawo wa Hong Kong matsaloli da yawa.
Kamar yadda aka ambata a cikin wannan talla kan yada shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic a Hong Kong, mazauna Hong Kong ba su mai da hankulansu kan wata gasa kawai ba. Domin yin shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic, Hong Kong ta kafa kamfanin musamman da ya jagoranci ayyukan shiryawa. Lin Huanguang, shugaban wannan kamfani ya ce,'A idon kamfaninmu da kuma hukumar Hong Kong, lokaci shi ne kalubale mafi girma a gare mu. Amma yanzu ma iya cewa, mun gudanar da ayyuka yadda ya kamata a daidai bisa ajandar da muka tsara a da.'
Mr. Chang Wei, babban darektan sashen kula da shirin sukuwar dawaki na gasar wasannin Olympic ya yi mana bayani da cewa, a watan Yuni na wannan shekara, Hong Kong ta jure mahaukaciyar guguwa mafi mugu. Abin gaskiya ya nuna cewa, filayen gasa sun jure wahalhalu. Mr. Chang ya ce,'Bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, mun gano cewa, a cikin filayen wasan, babu ruwa ko kadan. Ruwan ya iya shiga cikin kasa cikin sauri. Mun yi la'akari da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma mahaukaciyar guguwa da mu kan gamu a ko wane watan Agusta, ruwa ya iya shiga cikin kasar da ke cikin filayen wasanmu cikin sauri, babu ruwan da aka tattara a filayen wasanmu.'
1 2 3
|