
Mr. Sanjeev Gupta ya ce, a cikin kasashe 150 da rahoton IMF ya shafe, kusan kashi 50 cikin kashi 100 sun kashe kashi 0.6 cikin kashi 100 na dukkan yawan kudin da suka samu daga wajen samar da kayayyaki wato GDP daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2008 wajen gudanar da wadannan matakai, kuma kashi 1 cikin kashi 5 na wadannan kasashe sun kashe 1 cikin 100 na GDP.
Farashin man fetur da farashin hatsi a nan gaba suna jawo hankulan duniya sosai. Mr. Thomas Helbling wani gwani na hukumar IMF ya ce, saboda akwai batutuwa da yawa wadanda ba a tabbatar da su, ana fuskantar matsananciyar makoma a nan gaba.
Mr. Dominique Strauss-Kahn shugaban hukumar IMF ya ce, ana bukatar hadin gwiwa a tsakanin bangarori dabam daban na duniya, ciki har da gwamnatoci na kasashe dabam daban, da kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin taimako. Ya ce, "Babu magani zai iya warware wannan matsala har adaba. Kasashe dabam daban suna cikin halaye dabam daban. Aikin hukumar IMF shi ne samar da shawarwari mai daidaita ga kasashe dabam daban, da kuma samar da kudi idan akwai bukata. Amma ko shakka babu ana bukatar kokari da hadin gwiwa daga bangarori dabam daban na duniya." 1 2 3
|