
Ran 1 ga wata a Washington, hukumar IMF ta bayar da rahoto na farko na nazarin da ta yi kan karuwar farashin man fetur da hatsi na duniya. A cikin wannan rahoto, an yi nuni da cewa, ayyuka mafi muhimmanci da kasashen duniya ke fuskanta su ne samar da abinci ga mutane masu talauci, da kiyaye zaman karko na tattalin arzikin duniya daga manyan fannoni. Yanzu ga labarin da wakiliyarmu Madam Wang Shanshan ta ruwaito daga Washington.
Rahoton da hukumar IMF ta yi ya yi bincike kan tattalin arziki na kasashe 150 tun daga shekarar 2006. ya yi nuni da cewa, ana fuskantar da matsalar karuwar farashin kayayyaki cikin sauri tun bayan matsalar hauhawar kudi da ta faru a shekaru 70 na karni na 20. Farashin man fetur ya karu daga dolar Amurka 30 a ganwa a shekarar 2003 zuwa dolar Amurka 140 a ganwa a yanzu. Kuma farashin abinci ya fara karu daga shekarar 2006, kuma farashin shinkafa da mai sun karu da yawa.
Mr. Dominique Strauss-Kahn shugaban hukumar IMF ya ce, tattalin arzikin duniya yana faskantar kalubale sosai. Ya ce, "Wannan wani babban kalubale sosai ne. ko da yake akwai bambanci a kasashe dabam daban, amma kasashe da yawa suna fuskantar da barazana iri daya, ayyuka mafi muhimmanci a yanzu su ne samar da abinci ga mutane masu talauci, da kuma rike zaman karko na tattalin arziki daga manyan fannoni."
1 2 3
|