Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 17:55:44    
Hukumar ba da lamuni ta duniya ta IMF ta bayar da rahoton karuwar farashin man fetur da hatsi

cri

Madam Patricia Alonso-Gamo mataimakiyar direkatar ofishin nazarin bunkasuwa da manufofi na hukumar IMF ta ce, karuwar abinci da man fetur sun sanya kasashe da yawa sun sami matsala. Ta ce, "kasashe da yawa suna fuskantar da matsala a sakamkon halin matsi da suke ciki." Ta jadadda cewa, wasu kasashe suna shan wahala sosai saboda karuwar farashin hatsi da man fetur, amma wasu kasashe kamar kasashen da ke fitar da man fetur suna cin riba sosai daga wannan. Game da tattalin arziki na dukkan sassan duniya, ba shakka hauhawar kudi tana barazana ga fannonin kawar da talauci, da samar da isassen abinci, da kiyaye zaman karko na tattalin arzaiki daga manyan fannoni.

Mr. Sanjeev Gupta wani kwarare na ofishin harkokin kudi na hukumar IMF ya ce, gwamnatoci na kasashe dabam daban sun riga sun dauki matakai domin tinkarar matsalar hauhawar kudi. Ya ce, "Gwamnatoci na kasashe dabam daban sun riga sun dauki matakai iri iri domin tinkarar matsalar karuwar farashin hatsi da man fetur, manyan matakan da suka dauka su ne rage harajin man fetur da hatsi, da kara samar da kudin rangwame, da kara ba da albashi da kudin fensho."


1 2 3