Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-07-02 15:35:09    
Kasar Sin ta soma ayyukan gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin

cri

Kabilun kasar Sin suna da al'adar yin bikin nuna girmamawa ga kakani-kakaninsu, wani shahararen dan masana'antu na Hongkong Mr Zeng Xianzi wanda shi ne dan zuri'ar bayan mashahurin Zengzi na zamani aru aru ya bayyana cewa, gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin na da ma'ana sosai. Ya ce, na zo daga Hongkong, ni ne jikar zuri'a ta 74 ta Zengzi . A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, na tafi birnin Jining da ke lardin Shangdong don halartar bikin nuna girmamawa ga kakani-kakaninmu Zengzi da kakani-kakanin malaminmu Conficius a kowace shekara. A kowane karon da na halarci bikin, sai ya yi mini tasiri sosai. Tunanin Conficius ya ba da tasiri ga kasar Sin wajen raya zamantakewar al'umma cikin duban shekaru, a yau dai, Conficius ya riga ya zama alamar nuna alfahari ga 'ya'yan kasar Sin a duk duniya. A garin Conficius da Zengzi da Mengzi, an gina birnin da ke iya alamanta al'adun kasar Sin, ko shakka babu za a sami goyon baya da taimako daga Sinawan da ke zama a kasashen waje.


1 2 3