Kwanan baya, an yi shelar soma ayyukan gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin kuma aka yi shirin nan cikin shekaru 6 da suka wuce, ana soma neman shirye-shiryen tsara fasalin kago sabbin abubuwa na dukkan fannoni da na manyan yankunan da za a gina da na ayyuka na farko da za a gina ta hanyar ba da kyaututuka, lokacin neman shirye-shiryen daga ranar 1 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Satumba. Za a yi nunin shirye-shiryen tsara fasali a lokacin da za a yi bikin al'adun Conficius a garin Conficius wato Qufu da ke lardin Shangdong a shekarar da muke ciki.
Shahararrun masu kimiyya da mutane masu kishin kasa 69 na kasar Sin ne suka gabatar da shawarar shirya ayyukan gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin a karo na farko. Bisa shirin da aka yi, an bayyana cewa, za a gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin a birnin Jining na lardin Shandong . Inda za a aiwatar da shirin shi ne wani wuri mai suna Jiulongshan da ke tsakanin shahararrun birane wajen al'adu da tarihi , wato tsakanin birnin Qufu da Zoucheng ke nan. An bayyana cewa, Fuxi da Yandi da Huangdi da Shaohaodi da Yao da Shun da Yu da sauransu wadanda suka fara wayewar kasar Sin sun taba bari abubuwan tunawa a wurin. An haifi Conficius mai kafa akidar Conficius a gabashin tsaunin Jiulongshang, kuma an haifi wami muhimmin mutum mai bin akidar Conficius mai suna Mengzi a yammacin tsaunin, a wurin, gine-ginen zamani aru aru da kayayyakin tarihi na zamani aru aru suna da yawa, an riga an mayar da su don su zama manyan abubuwan da ke iya alamanta al'adun kasar Sin tun tuni. Direktan kwamitin gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin Mr Jiang Daming ya bayyana cewa, gina biranen da ke iya alamanta al'adun kasar Sin shi ne yin manyan ayyukan raya al'adu don yadada nagartattun al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma kara inganta karfin hada duk kasar Sin ta hanyar al'adu. An tsai da cewa, za a aiwatar da ayyukan a garin Conficius da Mengzi, wato birnin Jining, za a yi nunin karfi mai farin jini na al'adun kasar Sin. Tsaunukan Jiulongshan suna hada da manyan koluluwa guda 13 tare da tsawonsu na kilomita 5, inda an sami tatsuniyoyi masu ban mamaki sosai, sa'anan kuma a tsakanin tsaunukan, da akwai gine-ginen tarihi da kayayyakin tarihi da yawa.
1 2 3
|