Jama'a, ko kuna sane da cewa, kungiyar wasan iyo ta Australiya ta yanzu na kunshe da 'yan wasa 42, kuma 26 daga cikinsu, a karon farko ne za su shiga gasar wasannin Olympics. 'Yar wasa Libby Trickett za ta shiga gasar wasannin ne a karo na biyu. In ba a manta ba, a matsayin wata zakarar dake rike da kambun wasan iyo cikin 'yanci na tsawon mita 100 na mata a duniya a wacan lokaci, ita Libby Trickett ta sha kaye a gun gasa ta wannan wasa a gasar wasannin Olympics ta Aden ta shekarar 2004. Ta furta cewa: ' Lallai yanzu a shirye nake ga shiga wasannin Olympics. Amma a hakika, ban yi shiri sosai ba a shekarar 2004 domin kuwa na karo na farko ne na shiga wasannin Olympics. Ina cike da imanin cewa yanzu na samu goguwa sosai a gun gasanni yayin da nake kara fahimce ni da kaina a matsayin wata 'yan wasa'.
Daga bisani dai, Libby Trickett ta gaya wa wakilinmu cewa, za ta shiga gasanni a fannin ayyukan wasa iri uku a gun gasar wasanninn Olympics ta Beijing, wato wasan iyo da ake kira " Malam-Bude-Littafi" na tsawon mita 100, da wasan iyo cikin 'yanci na tsawon mita 50 a kuma wasan iyo cikin 'yanci na tsawon mita 100. Yanzu, 'yar wasa Libby Trickett da abokanta suna samun horo sosai na tsawon watanni hudu a birnin Brisbane da kuma birnin Cairns dake arewa maso gabashin kasar. Tana mai cewa: ' Yanzu muna kyautata ingancin horo da kara samun fasahohin yin gasa, ta yadda za mu gwada gwanintarmu mafi kyau a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing'.
Jama'a, ko kuna sane da cewa, 'yan wasa Libby Trickett mai shekaru 23 da haihuwa ta taba samun lambobin zinariya guda 3 a gun gasar cin kofin duniya ta wasan ninkaya a shekarar 2005. Sa'annan ta samu lambobin zinariya 4 a gun gasar cin kofin duniya ta wasan ninkaya ta gajeren zango a shekarar 2006 ; Kazalika, ta kwashe lambobin zinariya guda 5 a shekarar da ta gabata. Saboda haka ne, ake kiranta ' Sarauniyar wasan iyo' a duniyar yau.( Sani Wang ) 1 2 3
|