Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 15:25:49    
'Sarauniyar wasan iyo' ta duniya za ta shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

An labarta cewa, a gun gasar wasan iyo na duk kasar Austaliya da aka yi a kwanan baya, wassu 'yan wasa sun kuma karya matsayin bajinta na duniya a fannonin wasa guda 8. Wannan dai ya nuna babban karfin da Australiya take da shi na bunkasa wasan iyo. Amma a bayyane 'yar wasa Libby Trickett ta zama mai jagoran wannan kungiya bayan da 'yan wasa Ian Thorpe ya yi ritaya daga dandalin wasan iyo. A farkon gasar da aka gudanar, ta karya matsayin bajinta na duniya a fannin wasan iyo cikin 'yanci wato Free Style na tsawon mita 100 na mata da dakika 52 da digo 88, wanda 'yar wasa mai suna Britta Steffens daga kasar Jamus take rike da shi; wato ke nan 'yar wasa Libby Trickett ta zamo ta farko da ta kammala irin wannan wasa na tsawon mita 100 na mata cikin kasa da dakika 53 a duniya. Ban da wannan kuma kwanaki biyu bayan wannan lokaci, ta karya matsayin bajinta na duniya a wasan iyo cikin 'yanci na tsawon mita 50 na mata da dakika 23 da digo 97, maimakon dakika 24 da digo 09 da 'yar wasa Marleen Veldhuis daga kasar Holland ta kirirko cikin makon da ya wuce.

'Yar wasa Libby Trickett ta sa ran alherin cewa kungiyar wasan Iyo ta Australiya za ta samu maki mai kyau a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing da za a gudanar nan gaba kadan. Libby Trickett ta furta cewa: 'Lallai muna da babban karfi wajen samun lambobin zinariya domin muna da nagartattun 'yan wasa da yawa, wadanda za su karawa tare da sauran 'yan wasan iyo daga kasashe daban-daban a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing. A ganina, a yanzu haka dai, kungiyar Australiya tn kasancewa wata kungiya ce mafi karfi a cikin tarihi'.


1 2 3