Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-20 15:25:49    
'Sarauniyar wasan iyo' ta duniya za ta shiga gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, an kafa kungiyar wasan iyo ta kasar Australiya a hukumance bayan da aka kawo karshen gasar cin kofin duk kasar ta wasan iyo a karshen watan Maris na shekarar da take tafe. Wadanda suka shiga gasar sun hada da mashahuran 'yan wasa da dama na duniya. 'yar wasa mai suna Libby Trickett tana daya daga cikinsu. A gun gasar da aka gudanar a wannan gami, ta sami lambobin zinariya guda uku wato na wasan iyon da ake kira ' Malam-bude-littafi' na tsawon mita 100, da wasan iyo cikin 'yanci wato Free Style na tsawon mita 50 da kuma na mita 100 na mata. Saboda haka ne dai, aka lakaba mata ' Sarauniyar iyo' ta duniya. A yayin da Madam Libby take karbar ziyarar da wakilinmu ya yi masa, ta fadi cewa, za ta yi iyakacin kokarin samun kyakkyawan maki a gun gasar wasannin Olympics da za a gudanar a birnin Beijing na kasar Sin.

Sanin kowa ne, kungiyar kasar Australiya, wata kungiya ce mai karfi a dandalin wasan iyo na duniya. In ba a manta ba, tuni a shekarar 2004 lokacin da ake gudanar da wasannin Olympics na Aden a kasar Girka, kungiyar Australiya ta kwashe lambobin zinariya guda 7 bisa jagorancin shahararren dan wasan iyo Mr. Ian Thorpe, wato ke nan ta samu maki mafi kyau a gun wasannin Olympics na gabata da aka gudanar a waje da kasar din.


1 2 3