Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 14:33:28    
Kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin na daidaita sabuwar kalubalen da take fuskanta cikin natsuwa

cri

A 'yan kwanakin nan da suka wuce, Liu Xiang bai kammala gasa ba saboda jin rauni da kuma yin fawul a cikin gasannin da kungiyar IAAF ta shirya a biranen New York da Eugene na kasar Amurka. Ban da wannan kuma, Robles ya karya matsayin bajimta na duniya. Mutane sun nuna damuwa kan makomar Liu Xiang a gun gasar wasannin Olympic. Ko Liu Xiang ya sami sauki? Ko zai kyautata halinsa a gun gasar wasannin Olympic? Game da irin wannan damuwa, Mr. Feng ya kara da cewa, dalilin da ya sa Liu Xiang ya janye jikinsa daga gasar ba da babbar kyauta da kungiyar IAAF ta shirya a New York shi ne domin yana damuwar cewa, watakila irin wannan gasa mai zafi za ta tsananta rauninsa. A gaskiya bai ji rauni mai tsanani ba, shi ya sa rauninsa ba zai dame mutane ba.

Kazalika kuma, Mr. Feng ya yi karin bayani da cewa, bayan da ya kammala gasanni a New York da Eugene, Liu Xiang ya riga ya dawo kasar Sin domin ci gaba da aikin horaswa. Bisa shirin da aka tsara a yanzu, an ce, kafin shirin wasan guje-guje da tsalle-tsalle na gasar wasannin Olympic ta Beijing, Liu Xiang zai ci gaba da yin aikin horaswa a gida, ba zai yi gasa a kasashen waje ba.(Tasallah)


1 2 3