Ran 13 ga wata da sassafe bisa agogon Beijing, Dayron Robles, dan wasan gudun kataren shinge mai tsawon mita 110 da ya zo daga kasar Cuba ya karya matsayin bajimta na duniya a cikin gasar ba da babbar kyauta da hadaddiyar kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya wato IAAF ta shirya a birnin Ostrava na kasar Czech, makinsa shi ne dakikoki 12 da 87. Dan wasa Liu Xiang na kasar Sin shi ne ya rike da matsayin bajimta na duniya na da a cikin gasar gudun ketaren shinge mai tsawon mita 110 ta maza bayan da ya sami nasara a birnin Lausanne na kasar Switzerland a watan Yuli na shekarar 2006 da dakikoki 12 da 88. Ko nasarar Robles za ta yi illa ga Liu Xiang da ya nemi samun lambar zinariya a cikin shirin gudun ketaren shinge mai tsawon mita 110 a gasar wasannin Olympic ta Beijing? A lokacin da yake zantawa da wakilinmu, Feng Shuyong, babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ya bayyana ra'ayinsa.
A ganinsa, nasarar da Robles ya samu, wato karya matsayin bajimta na duniya, ba ta ba kungiyar kasar Sin mamaki sosai ba. Amma kungiyar kasar Sin ta ji mamaki kadan saboda ya sami irin wannan babban ci gaba a daidai lokacin da ya rage misalin watanni 2 kawai da bude gasar wasannin Olympic. Ya ce,'A gaskiya, nasararsa ba ta ba mu mamaki kwarai ba. Robles ya fara nuna karfinsa tun bayan karshen watanni 6 na shekarar 2006. Bayan gasannin da aka yi a shekarar bara, ya kara inganta karfinsa kwarai. A ganinmu, in ya kasance hali mai kyau, bai gamu da matsala ba, to, yau da gobe zai karya matsayin bajimta na duniya. Shi ya sa tun can da mun yi hasashen nasararsa. Amma ba mu kimanta cewa, ya karya matsayin bajimta na duniya kafin gasar wasannin Olympic ba. Na ji mamaki kadan da jin wannan labari.'
1 2 3
|