Kafin Robles ya karya matsayin bajimta na duniya, akasarin ra'ayoyin jama'a na mayar da Liu Xiang na kasar Sin da ya zama wanda ya fi nuna karfi wajen samun lambar zinariya a gasar wasannin Olympic ta Beijing. Amma nasarar Robles ta kawo wa Liu Xiang babbar matsin lamba. Shi ya sa Mr. Feng yake ganin cewa, nasarar da Robles ya samu bai kasance abu maras kyau ga Liu Xiang ba. Mr. Feng ya ce,'Na riga na tuntubi Sun Haiping, wanda ke horar da Liu Xiang. Muna ganin cewa, wannan na kasance abu mai kyau. A gaskiya, har kullum Liu Xiang da Robles suna cikin halin kaka-ni-ka-yi. Yanzu Robles ya sami irin wannan nasara, ya karya matsayin bajimta na duniya, a ganina, Liu Xiang ya fitar da kansa daga matsin lamba da ake danka masa. A kalli zai sami fifiko a tunani.'
Amma Robles ya yi fintikau kamar hakan a watanni 2 kafin gasar wasannin Olympic, ko zai iya ci gaba da yin fintikau a cikin gasar wasannin Olympic ko a'a? Game da wannan, Mr. Feng ya nuna cewa,'Babu wanda zai iya yin hasashen wannan ba. Ko wane dan wasa ya sha bamban da juna, amma dukkansu sun gaza wajen yin fintikau a cikin dogon lokaci. Robles ya karya matsayin bajimta na duniya ne a daidai lokacin da yake cikin hali mai kyau. Sa'an nan kuma, a cikin gasar gudun ketaren shinge mai tsawon mita 110, yadda abokan takararsa suke yi ya kan ba da tasiri kan wani dan wasa.'
1 2 3
|