A waje daya kuma kallon talabijin kullum zai iya rage karfin idanun yara da kuma karuwar nauyin jikinsu, da daina yin barci yadda ya kamata, da kuma rashin sha'awar yin cudanya da sauran mutane. Sabo da haka zai yi illa sosai ga lafiyar jiki da tunanin yara.
Bisa sakamakon binciken da Dr. Sigman ya gudanar, an ce, an yi mamaki sosai da yawan lokutan da yaran kasar Birtaniya ke kashewa wajen kallon talabijin. Game da yaran da shekarunsu ya kai 6 da haihuwa kawai, matsakaicin yawan shekarun da suka kashe wajen kallon talabijin ya zarce shekara guda. Sabo da haka, Dr. Sigman ya yi kira ga gwamnatin kasar Birtaniya da ta dauki tsauraran matakai don tallafa wa yara wajen rage yawan lokacin kallon talabijin, ta yadda za su iya samun lafiyar jiki.
To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao) 1 2 3
|