Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-18 14:20:55    
Kallon talabijin kullum zai iya yin illa ga yara wajen cin abinci

cri

A kwanan nan, manazarta na jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun gabatar da wani rahoto ga kungiyar kula da zuciya ta kasar, inda suka bayyana cewa, lokacin da yara suke kallon talabijin, su kan yi kalaci sosai. Kuma sannu a hankali za su kirkiri dabi'a maras kyau ta cin abinci maras kyau, wadda za ta haddasa karuwar yawan nauyin jiki.

Manazarta sun gudanar da wani bincike ga yara 1203 da shekarunsu ya kai 3 da haihuwa kan abubuwan da suke yi lokacin da suke kallon talabijin. Daga baya kuma sun gano cewa, kusan dukkan yara su kan sha abinsha ko cin abinci lokacin da suke kallon talabijin. Sabo da wadannan yara sun yi kalaci maras kyau fiye da kima lokacin da suke kallon talabijin, shi ya sa ba safai su kan so cin abinci a lokcin cin abinci yadda ya kamata ba. Sabo da haka kuma yawan 'ya'yan itatuwa da kuma kayayyakin lambu da dai sauran abinci masu gina jiki da yaran da suke son kallon talabijin su kan ci ya yi kadan idan an kwatanta shi da na yaran da ba su son kallon talibiji.

Ban da wannan kuma rahoton ya bayyana cewa, idan tsawon lokacin kallon talabijin ya karu, sai yawan abinci da yara suka ci ya karu, kuma yawan sinadarin calorie da suke samu daga abinci ya karu, a waje daya kuma yawan lokacin motsa jiki ya ragu, sabo da haka yaran da su kan yi kallon talabijin suka fi saukin samun kiba. Bugu da kari kuma manazarta sun bayyana cewa, idan yawan lokacin kallon talabijin ya karu da awa guda, to yawan sinadarin calorie da yara suka samu daga abinci zai karu da 46. A kwana a tashi, wannan zai iya yin illa ga lafiyar jikinsu.


1 2 3