Da farko, ya kamata a samu dalilan da suka sanya cutar, daga baya kuma a dauki tsauraran matakai. Alal misali, game da mutanen da su kan sha giya sosai, ya kamata su daina shan giya. Game da mutanen da suke kamuwa da cutar sukari, ya kamata su rage yawan sukari da ke cikin jininsu. A takaice dai, kau da dalilan da suka sanya cutar zai ba da taimako wajen warkar da cutar taruwar kitse a hanta.
Haka kuma ya kamata a daidaita tsarin abinci, da kuma kara cin abincin da ke kunshe da sinadarin protein da Vitamin yayin da sukari kadan da kuma kitse kadan.
Ban da wannan kuma, ya kamata a kara yin motsa jiki domin sa kaimi ga kashe yawan kitse da ke cikin jiki. Furofesa Zhang Hongfei ta yi gargadi ga mutane masu matsakaitan shekaru da haihuwa da kuma tsoffi, cewa
"lokacin da ake yin motsa jiki, ya kamata a dora muhimmanci kan yawan motsa jiki, da hanyar motsa jiki, da kuma lokacin motsa jiki. A takaice dai, ya kamata a yi motsa jiki sau biyu a ko wace rana, kuma a yi haka rabin awa a ko wane karo har samun gumi kadan. Idan an yi motsa jiki kamar haka har sau 3 zuwa 5 a ko wane mako, to za a iya hana barkewar cutar taruwar kitse a hanta."(Kande Gao) 1 2 3
|