A cikin asibitoci daban daban na kasar Sin, a kan gamu da mutanen da suka kamu da cutar taruwar kitse a hanta. Ya zuwa yanzu cutar ta riga ta zama cutar hanta mafi tsanani ta biyu a kasar Sin wadda a kan fi samun yawan mutanen da suka kamu da ita ban da cutar kunburin hanta, haka kuma ita muhimmin dalili ne da ya sanya cutar taurarewar hanta. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, a shekara ta 2001, yawan mutanen da suka kamu da cutar taruwar kitse a hanta a kasar Sin ya kai kashi 19.3 cikin dari, kuma wannan jimla ta karu zuwa kashi 25.3 cikin dari a shekara ta 2003. Bisa halin da duk fadin kasar Sin ke ciki, an gano cewa, mutanen da suke kamuwa da cutar suna da yawa, kuma wannan jimla tana ta samun karuwa.
Game da wadanne mutane suka fi saukin kamuwa da cutar taruwar kitse a hanta, furofesa Zhang Hongfei ta asibiti mai lamba 302 na sojojin kasar Sin ta bayyana cewa,
"A hakika dai, a kan kamu da cutar taruwar kitse a hanta bisa dimbin dalilai. Na farko shi ne dabi'ar zaman rayuwa maras kyau, kamar cin abinci fiye da kima yayin da yin motsa jiki ya yi kadan. Na biyu shi ne illar da magunguna ke yi wa hanta, ban da wannan kuma akwai wasu dalilan halitta, alal misali cutar kunburin hanta za ta haddasa cutar taruwar kitse a hanta."
1 2 3
|