Cutar taruwar kitse a hanta wata cutar hanta ce ta yau da kullum, idan an iya samun jiyya cikin lokaci, to za a iya warkar da ita. Sabo da haka samun jiyya da wuri ya taka muhimmiyar rawa wajen hana tsanantar cutar da kuma kyautata aikin rigakafin cutar. Amma ta binciken da aka gudanar, an gano cewa, dimbin mutanen da ke kamuwa da cutar ba su mai da hankali sosai a kanta.
"A ganina, cutar taruwar kitse a hanta ba wata cuta mai tsanani ba ne."
"Idan an mai da hankali a kan abinci, wato shan giya kadan, shi ke nan za a iya shawo kan cutar."
Amma a hakika dai, idan ba a iya warkar da cutar taruwar kitse a hanta cikin lokaci ba, to za a samu mummunan sakamako, har ma za a kamu da cutar kumburin hanta da cutar taurarewar hanta har ma sankarar hanta.
To, idan an kamu da cutar taruwa kitse a hanta, yaya za a yi wajen warkar da ita?
1 2 3
|