Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 14:19:23    
Kasashen Afirka sun dauki matakan yaki da hauhawar farashin hatsi

cri

A waje daya kuma, kungiyoyin shiyya-shiyya da hukumomin kudi na shiyya-shiyya na Afirka sun kara karfin tallafawa aikin gona. A kwanan baya, kawancen tattalin arziki da kudi ta kasashen yammacin Afirka sun shirya wani taron musamman a birnin Abidjan, babban birnin tattalin arziki na kasar Kwadivwa, inda ta sanar da cewa, za ta zuba kudaden da yawansu zai kai dolar Amurka miliyan 240 a kasuwannin yankunan yammacin Afirka. Bugu da kari kuma, bankin raya yammacin Afirka zai kebe rancen kudin African Franc biliyan 100 a kowace shekara a cikin shekaru 3 masu zuwa domin tallafawa shirye-shiryen noma na yankunan yammacin Afirka. A ran 2 ga watan Mayu, bankin raya Afirka ya dauki alkawarin cewa, zai sake samar da rancen kudin da yawansu zai kai dalar Amurka biliyan 1 domin tallafawa shirye-shiryen noma na Afirka.

Haka kuma, manazarta sun nuna cewa, wannan rikicin karancin abinci da ya auku a duk fadin duniya ya yi wa kasashen Afirka kashedi. Sun ce, ya kamata kasashen Afirka su yi koyi da fasahohi da kasar Sin ta samu kan yadda take raya aikin gona da tabbatar da samar da isashen abinci. Wannan zai zama wata sabuwar damar yin hadin guiwa a fannin aikin gona a tsakanin kasashen Afirka da Sin.

Manazarta suna ganin cewa, dalilan da suka sa kasar Sin da ta gudu daga wannan rikicin abinci su ne, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin samar da shinkafa da kanta. Sabo da haka, sauyin kasuwannin hatsi na duniya bai kawo illa ga kasuwannin hatsi na cikin gidan kasar Sin ba, kuma kasar Sin ta samu ikon tabbatar da farashin shinkafa a kasuwannin cikin gida. Ban da wannan, lokacin da farashin shinkafa yake samun hauhawa a kasuwannin duniya, dalilan da suka sa farashin kasuwar shinkafa ta cikin gidan kasar Sin bai samu canzawa sosai ba su ne kasar Sin ta bayar da jerin manufofin moriyar aikin gona, kuma take da karfin sarrafa tattalin arzikinta daga dukkan fannoni.


1 2 3