Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 14:19:23    
Kasashen Afirka sun dauki matakan yaki da hauhawar farashin hatsi

cri

Yanzu ana fuskantar batun hauhawar farashin hatsi a duk fadin duniya. Game da wannan matsala, kasashen Afirka sun dauki matakan yaki da shi bi da bi.

Da farko dai, bi da bi ne kasashen Afirka suka kara yawan kudaden da suke zubawa kan aikin gona da sauran masana'antun da ke da nasaba da aikin gona domin jawo manoma da su mai da hankulansu kan noman hatsi da kokarin karin yawan hatsin da za su iya yin girbi. Alal misali, kasar Kenya ta samar da rancen kudin da za a biya kudin ruwa kadan ga manoma da kananan masana'antun aikin gona, ta kuma samar da ire-iren shuke-shuke da kayyakin aikon gona ga wuraren da suke fama da bala'u daga indallahi domin taimaka musu wajen farfado da aikin kawo albarka. Gwamnatin kasar Saliyo ta samar da injunan noma ga manoma, ta kuma nemi hukumomin aikin gona da na tabbatar da samar da hatsi da gandun daji da su dauki matakan kyautata hanyoyin noma na zamani da manoma suke mallaka. A waje daya kuma, gwamnatin Saliyo ta bayar da wasu manufofi masu gatanci ga wadanda suke sarrafa gandun noma ta hanyar kasuwanci.

Haka kuma wasu kasashen Afirka sun dauki matakan kara shigar da hatsi daga kasashen waje ko rage yawan hatsin da ake fitar da shi zuwa kasashen waje domin tabbatar da samar da hatsi a kasuwannin gida. Alal misali kasashen Kenya da Nijeriya sun kebe kudade masu dimbin yawa wajen shigar da hatsi. A waje daya kuma, kasashen Nijeriya da Gabon da Kwadivwa sun sanar da cewa, za su dakatar da buga harajin kwastan kan shinkafa da garin alkama da man girki da ake shigar da su daga kasashen waje. Kasashen Zambiya da Madagascar da Tanzania sun bayar da manufofin kayyade fitar da hatsi zuwa kasashen waje.


1 2 3