Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-17 14:19:23    
Kasashen Afirka sun dauki matakan yaki da hauhawar farashin hatsi

cri

Bugu da kari kuma, kasashen Afirka sun kara tallafawa mutane wadanda suke samun kudin shiga kadan. A kwanan baya, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta tabbatar da wasu kayayyakin masarufi da ba za a buga haraji a kansu ba domin taimakawa matalauta da su tsirar da kansu daga mawuyacin halin da suke ciki yanzu.

Sannan kuma, wasu kasashen Afirka sun aiwatar da kayyade farashin kayayyakin masarufi. Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da jerin manufofin kayyade farashin abinci, kamar su ba za a buga harajin kwastan kan kayayyakin masarufi da ake shigar da su daga kasashen waje ba, kuma za ta soke harajin da take bugawa kan wadanda suke sayar da irin wadannan kayayyakin masarufi domin raguwar farashin abinci.

Bugu da kari kuma, kasashen Zambiya da Kwadivwa da Gambiya sun kara karfin yin yaki da laifin shigi da ficin hatsi ba bisa doka ba da laifin adana hatsi domin jiran damar neman karin riba.


1 2 3