Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 15:03:49    
An samu saurin ci gaba fiye da ko wane lokaci na da wajen likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet ta kasar Sin

cri

A jihar Tibet, aikin hada magungunan gargajiya na jihar shi ma ya samu saurin ci gaba fiye da ko wane lokaci na da, ma'aikatun hada magunguna suna gudanar da ayyukansu ta hanyar hada tsarin aikin kawo albarka na gargajiya da kimiyya da fasaha na zamani. Yanzu da akwai magungunan gargajiya na Tibet wadanda nau'o'insu sun wuce 20, wadanda kuma aka rubuta sunayensu cikin "Babban littafin magungunan Jamhuriyar jama'ar Sin", kuma da akwai nau'o'in magungunan 336 wadanda ingancinsu ya kai ma'aunin da gwamnatin kasa Sin ta tsayar, kuma ana sayar da su ga sauran wuraren kasar Sin da kasashen waje. Shehun malami Nyima Tsering na kolijin koyon ilmin likitanci ta jihar Tibet ya bayyana cewa,

"An samu manyan sauye-sauye fiye da ko wane lokaci na da wajen harkokin ba da ilmi da kiwon lafiya, da akwai mutanen kasashe da yawa wadanda suka rubuto mana wasiku cewa, suna fatan za su iya samun damar koyo da yin binciken likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet."

Yawan masana'antun hada magungunan gargajiya na jihar Tibet sun riga sun karu daga daya na kafin lokacin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje zuwa 19 na yanzu, yawan nau'o'in magungunan da aka hada ya wuce 360. Domin biyan bukatun kasuwanni, wadannan masana'antu kuma sun hada magunguna na sabon salo cikin har da capsule da ruwan magani da kwayoyin magani da filasta ta hanyar hada likitancin gargajiya na Tibet da fasahar zamani.


1 2 3