Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 15:03:49    
An samu saurin ci gaba fiye da ko wane lokaci na da wajen likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Likitancin kabilar Tibet wani kashi ne daga cikin likitancin gargajiya na kasar Sin, wanda yake da tarihi na fiye da shekaru 2300. A jihar Tibet, an riga an kafa tsarin yin likitanci da magungunan gargajiya na kabilar Tibet a dukkan gundumomi da garuruwa, yanzu da akwai manyan hukumomin likitancin Tibet fiye da 10 a jihar, kuma da akwai dubban ma'aikata da ke aiki a cikin su. To, jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani game da ci gaban da aka samun wajen likitanci da magungunan gagajiya na jihar Tibet ta kasar Sin.

Shehun malami Dondrup, shugaban ofishin binciken kimiyya da fasaha na likitanci da magangunan gargajiya na jihar Tibet, kuma yana daya daga cikin daliban da suka samu digiri wajen likitancin Tibet a karo na farko na bayan samun 'yancin jihar a shekaru na 50 na karnin da ya wuce. Cikin shekaru 18 da suka wuce, kullum yana dukufa kan aikin warkar da marasa lafiya, da ba da darasi, da yin binciken kimiyya, yana shan aiki a kowace rana. Ya ce,

"A da, yawan daliban da suka nazarci likitancin gargajiya na Tibet ya kai 300 ko fiye kawai, amma yanzu wannan adadi ya wuce 1400, wato ana cin gadon likitancin gargajiya da kyau."


1 2 3