Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 15:03:49    
An samu saurin ci gaba fiye da ko wane lokaci na da wajen likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Domin kara tallafi da kuma bunkasa likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet, an bude asibitin Tibet da ke nan birnin Beijing a shekarar 1992. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, wannan asibiti ya tattara shahararrun likitoci 'yan kabilar Tibet da suka zo daga wurare daban-daban, kuma an shigar da sashen warkar da ciwace-ciwacen hanyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, da na ciwon sukari da ciwon hanta na wannan asibiti cikin jerin sunayen muhimman sassan likitanci bisa matsayin kasa. Shehun malami Nyima Tsering na cibiyar binciken likitancin gargajiya na Tibet ya bayyana cewa,

"A halin yanzu, likitanci da magungunan gargajiya na jihar Tibet sun samu manyan sauye-sauye idan an kwatanta su da na kafin samun 'yancin jihar. Wajen fannin ba da ilmi ana iya cewa, kusan babu muhimmin wurin ba da ilmin likitanci da magungunan gargajiya kafin lokacin samun 'yancin kan jihar Tibet. Amma yanzu, musamman ma bayan kafa muhimman wurarin ba da ilmi mai zurfi wajen likitanci da magungunan gargajiya na Tibet, an samu ci gaba daga fannoni daban-daban ciki har da girman sikeli da kuma sharudan ba da ilmi, da halayyan malaman koyarwa."

An ce, yawan bakin da suka kawo ziyara asibitin Tibet da ke nan birnin Beijing ya wuce dubu 20 a kowace shekara. Bisa kididdigar da aka yi an ce, ya zuwa yanzu yawan marasa lafiya da suka je wannan asibiti domin ganin likitoci ya wuce miliyan daya, ciki har da mutane fiye da dubu 300 wadanda suka zo daga kasashe fiye da 60 na duniya da shiyyoyin Hongkong da Macao da Taiwan.


1 2 3