Ban da cewar manoman kasar Sin sun ci gajiyar alamun wurin noma wajen kara samun kudin shiga mai yawa, kuma sun sami babban taimako daga wajen alamun nan don fitar da amfanin gona zuwa kasashen waje. Malam Guo Qiuzhi ya kara da cewa, kafin rajistar alamun wurin noma, mun sha gamuwa da wahala wajen yin shawarwari tare da 'yan kasuwa na kasashen waje, dalilin da ya sa haka shi ne domin 'yan kasuwan ba su nuna amincewa sosai ga 'ya'yan itatuwanmu ba, amma yanzu al'amarin ya canju sosai. Ya ce, "a shekarar bara, yayin da 'yan kasuwa na kasashen Peru da Argentina suke yin shawarwari tare da mu, sun ji alamar wurin noman Pear ta Kuerlei da aka yi rajistarta ta zama shahararren tambarin amfanin gona a kasar Sin, sai sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar odar 'ya'yan itatuwan nan cikin sauri."
A hakika dai, sakamako da kasar Sin ta samu wajen kiyaye alamun wuraren noma abu ne da kasashe daban daban ke iya gani. A gun taro kan alamun wuraren noma na duniya da aka shirya a karshen watan Yuni da ya wuce, Madam Wu Yi, mataimakiyar firayim ministar kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin tana yin amfani da alamun wuraren noma wajen kiyaye amfanin gona da bunkasa su, don sa kaimi ga noman amfanin gona masu yawa da kara darajarsu, ta yadda za a kara wa manoma kudin shiga da raya kauyuka.
1 2 3
|