Alamun wuraren noma alamu ne da ke nuna wurare da aka samu amfanin gona da ingancinsu da kuma kwarjininsu. A cikin shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga kiyaye al'amun wuraren noma, don sa kaimi ga bunkasa aikin noma a kasar.
Wani irin 'ya'yan itatuwa masu zaki da ake kira "Pear" a Turance, wadanda ake nomawa a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin sun zama na farko wajen yin rajistar alamun wurin fitar da kayayyaki a kasar Sin. Malam Guo Qiuzhi, babban sakataren kungiyar masu noman irin wannan Pear ta Kuerlei ta garin Bazhou na jihar Xinjiang ya bayyana cewa, rajistar alamar wurin noman Pear ta Kuerlei ya kara wa manoman wurin kwarin guiwa wajen noman 'ya'yan itatuwan nan. Ya ce, "dama, manoma sun nuna damuwa da cewa, idan sun habaka filayen gonaki da suke noma 'ya'yan itatuwan, to, karuwar 'ya'yan itatuwan da suke samu zai sa farashinsu ya ragu, ta haka yawan kudin shiga da suke samu ma zai ragu. Amma a cikin shekarun nan uku da suka wuce, sun sayar da 'ya'yan itatuwan nan cikin sauki, 'yan kasuwa sun sayi duk 'ya'yan itatuwa masu inganci da suka noma, don haka manoman suna kara nuna himma sosai ga noman 'ya'yan itatuwan nan."
An ruwaito cewa, bayan da aka yi rajistar alamar wurin noman Pear ta Kuerlei, 'ya'yan itatuwan nan sun kara shahara, farashinsu ma ya karu, ta haka manoman wurin sun sami babbar fa'ida.
1 2 3
|