Ana yin shawarwari sau biyu a ko wace shekara a kasashen biyu bi da bi. Yanzu, an riga an yi shawarwari sau uku.
Ran 14 zuwa ran 15 ga wata na shekarar 2006, an yi shawarwarin na karo na farko a birnin Beijing. Bangarorin kasashen biyu sun yi shawarwarin kan batun "bunkasuwar kasar Sin da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin bisa manyan tsare-tsare". Bayan an kammala shawarwarin, Madam Wu Yi ta ce, "Ni da minista Paulson, da sauran wakilan kungiyoyin kasashen Sin da Amurka, muna ganin cewa, an sami nasara sosai a shawarwari na karo na farko, wannan zai ba da gudummawa ga huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin kasashen biyu."
Tun daga ran 22 zuwa ran 23 ga watan Mayu na shekarar 2007, an gudanar da shawarwari na karo na biyu a Washington, babban birnin kasar Amurka. Bayan an kammala shawarwarin, Mr. Paulson ya ce, "Yau mun sami ra'ayi iri daya kan hadin gwiwar da ke tsakaninmu a nan gaba daga fannoni dabam daban, ciki har da aikin hidima na kudi, da yin amfani da makamashi, da kiyaye muhalli, da kuma zirga-zirgar jirgin sama na jama'a. za mu cigaba da yin wannan shawarwari, kuma za mu cigaba da yin hadin gwiwa."
1 2 3
|