Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-16 11:46:44    
Tuna da shawarwarin tattalin arziki da kasashen Sin da Amurka suka yi bisa manyan tsare-tsare

cri

Tun daga ran 17 zuwan ran 18 ga wata birnin Anapolis na jihar Maryland na kasar Amurka, za a soma shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka na karo na hudu, Mr. Wang Qishan mataimakin firaministan kasar Sin da Mr. Henry M. Paulson ministan harkokin kudi na kasar Amurka za su jagoranci wannan shawarwari tare. A wannan lokacin da za a fara yin wadanan shawarwari, bari mu tuna da sakamakon da aka samu a shawarwari guda uku da suka gabata. Yanzu ga labarin da wakilanmu Madam Wang Qian ta ruwaito mana.

Shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare shi ne shawarwari mafi muhimmanci da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma su ne shawarwari mafi matakin koli da ke tsakanin manyan jami'an kula da harkokin tattalin arziki na kasashen biyu a tarihi. A ran 20 ga watan Satumba na shekarar 2006, Madam Wu Yi tsohuwar mataimakiyar firaminista ta kasar Sin da Mr. Paulson ministan harkokin kudi na kasar Amurka sun bayar da wata tarrayar sanarwa, inda suka sanar da cewa, an fara gudanar da tsarin shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Amurka.Madam Wu Yi ta ce, "Yan, Mr. Paulson da ni, mu sanar da wannan labari tare, wato an fara gudanar da tsarin shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Amurka. Wannan shi ne wani tsarin shawarwarin da aka kafa tsakanin kasa mai tasowa mafi girma da kasa mai cigaba mafi girma na duniya kan fannin tattalin arziki."


1 2 3