Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-06 16:10:17    
Zagayawa da fitilar wasannin Olympics a kasashen kasa da kasa ta gwada kyakkyawar surar birane ga duniya

cri

A karo na farko ne birnin Islamabad na Pakistan ta dauki nauyin mika fitilar wasannin Olympics. Jakadan kasar Sin dake a Pakistan Mr. Luo Zhaohui ya furta cewa: ' Zagaya fitilar wasannin da aka yi, ya kasance tamkar wata muhimmiyar dama ce ga gwamnatin Pakistan ta yanzu, wadda take cikin yanayin canjin tsarin siyasa. Tana kishin samun wannan dama don bayyana wa gamayyar kasa da kasa zaman karko da take da shi'.

Aminai 'yan Afrika, saboda dalilai iri daban-daban ne, mutane ke kasa fahimtar kasar Korea ta Arewa. Lallai mika fitilar wasannin Olympics a Pyongyang ya bude wata taga domin wannan kasa. Jakadan kasar Sin dake Korea ta Arewa Mr. Liu Xiaoming ya furta cewa: " Jama'ar Korea ta Arewa suna fatan ta wannan dama ne za a bayyana wa kasashen duniya nasarorin da suka samu wajen raya kasarsu".

Birnin Ho Chi Minh na kasr Vietnam, birni na karshe ne na ketare ,inda aka zagaya fitilar wasannin Olympics na Beijing. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na Vietnam Mr. Nguyen Danh Thai ya ce "hakan ya samar wa birnin na Ho Chi Minh damar rubuta birnin cikin littafin tarihi". A daya wajen, jakadan kasar Sin a Vietnam Mr. Hu Qianwen ya yi karin haske cewa: "Yanzu, Vietnam na da kyakkyawan yanayin siyasa da na tattalin arziki. Ko shakka babu, yin yawo da fitilar wasannin a birnin Ho Chi Minh zai yi tasiri mai kyau ga birnin da kuma kasar Vietnam baki daya".


1 2 3 4