Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a yanzu haka dai, ana zagaya fitilar wasannin Olympics na Beijing a cikin yankin kasar Sin. Amma kafin wannan, ta hannun masu dauke da fitilar wasanni kimanin 2,000 ne, aka gwada kyakkyawar surar birane 19 na nahiyoyi biyar ga duk duniya.
Mika fitilar wasannin Olympics na da babban tasiri. Mr.Yasin Aksoy, shugaban kwamitin rokon daukar bakuncin gasar wasannin Olympics na Istanbul ya furta cewa, birnin na Istanbul, wani kyakkyawan birni ne, wanda yake neman iznin shirya gasar wasannin Olympics. Mun mayar da zagaya fitilar wasannin a wannan gami a matsayin wata ishara mai kayatarwa dake akwai a cikin yunkurin neman iznin shirya gasar wasannin Olympics ta shekarar 2020.
Domin gwada kyakkyawar surar birnin na Istanbul, Mr.Aksoy shi kansa ne ya zama babban mai shiga tsakanin harkar mika fitilar wasannin Olympics ta Beijing. Jakadan kasar Sin a kasar Turkiyya Mr. Sun Guoxiang ya furta cewa: ' Dukkanin 'yan kasar Turkiyya suna fadin cewa, zagaya fitilar wasannin Olympics a kasarsu ya samar musu da wani kyakyawar damar gwada surar kasarsu da kuma surar birnin Istanbul, hakan ya aza tubali mai inganci ga takarar da birnin Istanbul take yi wajen rokon daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2020'.
1 2 3 4
|