Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:21:23    
Gandun daji na Shennongjia

cri

Bunkasuwar aikin yawon shakatawa ta kawo wa mazauna Shennongjia kudaden shiga da yawa. Amma karuwar yawan masu yawon shakatawa ta kawo wa muhallin halittu na wannan gandun daji matsin lamba kadan. Duk da haka, mazauna wurin sun mayar da kiyaye muhallin halittu a gaba da samun kudade. Har kullum hukumar wurin tana kula da kiyaye muhallin halittu da kuma namun daji masu daraja.

Domin samar da namun daji ire-ire fiye da dubu 1 lokacin hutu, da kuma kyautata muhallin halittu a gandun daji na Shennongjia, tun daga watan Janairu zuwa watan Maris na shekarar 2006, an dakatar da bude kofar gandun dajin ga masu yawon shakatawa. don haka, muhallin halittu na samun kyautatuwa sannu a hankali a gandun daji na Shennongjia, haka kuma, yawan namun daji na ta karuwa. A shekarar 2006, wasu shahararrun kwararru sun zo gandun daji na Shennongjia domin yin bincike, dukkansu sun darajanta kasancewar halittu iri daban daban da kuma cikakken muhallin halittu da kuma rashin sa kafar dan Adam a wannan gandun daji.


1 2 3