Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:21:23    
Gandun daji na Shennongjia

cri

Tun daga shekaru 1970, lalacewar muhalli na gandun daji na Shennongjia ta dawo hankulan gwamnatin Sin da kwararrun da abin ya shafa, shi ya sa aka kaddamar da hana cire itatuwa a wannan gandun daji tun daga watan Maris na shekarar 2000. A sakamakon kiyayewa daga dukkan fannoni har tsawon shekaru 8 ko fiye, fadin wuraren da aka dasa itatuwa ya kai misalin kashi 88 cikin dari bisa jimlar fadin gandun dajin. Kyautatuwar muhalli a gandun daji na Shennongjia ta samar wa namun daji na wurin kyakkyawan muhallin halittu.

Dukkan gandun daji na Shennongjia na cikin garkuwar manyan tsaunuka. Shi ya sa ko da lokacin zafi ya yi, ana jin sanyi da nishadi sosai a wurin. Iska mai sanyi na kan buga daga manyan tsaunukan. Masu yawon shakatawa suna iya more idanunsu da itatuwa masu tarin yawa. Haka kuma suna sauraren kukan namun daji iri daban daban da kuma amon ruwan da ke gangarowa a kwari. A shekarun baya da suka wuce, dimbin masu yawon shakatawa sun kawo wa gandun daji na Shennongjia ziyara.


1 2 3