Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:19:51    
Titin Hefangjie da ke birnin Hangzhou

cri

Sigogin musamman na titin Hefangjie ta fuskar tarihi sun jawo hankulan masu yawon shakatawa daga wurare daban daban na duniya. Yanzu fadin titin ya kai kadada misalin 13.6, ya fi nuna al'adun Hangzhou da suka fi nuna halayen musamman na wannan birni a harkokin tarihi da kasuwanci da zaman rayuwar fararen hula da kuma gine-gine. Yau a daidai lokacin da muke tattara labaru a wannan titi, Mr. Wei Chenghe, wani Basinne da yake zama a kasar Malaysia yana yawo a titin Hefangjie, ya nuna matukar yabo kan wannan titi. Ya ce,

'Wannan shi ne karo na farko da na kawo nan ziyara. A da ban yi tsammani da cewa, akwai irin wannnan kyakkyawan titi mai halayen musamman na gargajiya a nan ba. Na taba koyar da Sinanci, shi ya sa na san tarihin kasar Sin a wasu fannoni. A lokacin da nake yawo a kan wannan titi, sai ka ce, ina yawo a cikin wani fim game da 'yan kundunbala da ke da fasahar Kungfu. Na sayi wasu abubuwan takarda da aka kera da hannu. In akwai dama, ina so in sake kawo nan ziyara tare da iyalina. A gaskiya da kyar na gano wani wuri daban da ya yi kyan gani hakan. Musamman ma mu Sinawa mazauna kasashen waje mun sami damar kawo wa mahaifarmu ziyara, inda muka gano cewa, ana adana wasu abubuwan gargajiya yadda ya kamata, musamman ma kayayyakin da aka kera da hannu masu inganci. Wadannan gine-gine sun fi burge ni, haka kuma wadannan kayayyakin da aka kera da hannu. Masu fasahar gargajiya sun gwanance wajen kera irin wadannan abubuwa. Na yaba wa gada irin wadannan fasahohin gargajiya a nan gaba ainun.'

A halin yanzu, kwamitin harkokin titin Hefangjie ya tsara wani shiri daban, wato raya wannan titi da ya zama titin gargajiya na nishadi da mazauna Hangzhou za su iya yin ziyarar yau da kullum, ta haka wannan titi zai zama wani wuri inda kasuwanci da aikin yawon shakatawa za su sami yalwatuwa, kuma masu saye-saye na zamani za su yi maraba da shi, haka kuma zai iya nuna halayen musamman na gargajiya.


1 2 3