Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-06-03 15:19:51    
Titin Hefangjie da ke birnin Hangzhou

cri

Birnin Hangzhou yana bakin teku a kudu maso gabashin kasar Sin, tsawon shekarunsa ya kai fiye da 2200. Tun can da, Sinawa su kan ce, Hangzhou, sai ka ce aljannar duniyarmu. Ta haka mun iya gano yadda kyakkyawar Hangzhou take a zukatan Sinawa. Yau ma zan gabatar muku da titin Hefangjie da ke wannan birni. Wannan titi yana gindin shahararren tsaunin Wushan a Hangzhou, shi ne wani bangare na tabkin Xihu, wanda aka nemi shigo da shi cikin kayayyakin tarihi na al'adu na duniya. Titin Hefangjie na daya daga cikin titunan da suka fi nuna sigar musamman ta Hangzhou a harkokin tarihi da al'adu.

Tsawon muhimmin bangare na titin Hefangjie ya kai misalin mita 460, fadinsa ya kai misalin mita 12. Yau da shekaru fiye da 880 da suka wuce, mahukuntan zamanin daular Nansong ta mayar da Hangzhou a matsayin babban birninsa, titin Hefangjie shi ne cibiyar al'adu da tattalin arziki da kuma kasuwanci a wannan lokaci, inda kullum a kan sami rububin mutanen da ke kaiwa da kawowa. Yanzu a titin Hefangjie, ana adana wasu gine-ginen gargajiya, kuma gidajen da ke gefuna 2 na titin aka gina su ne da katako da fale-falen jinka, dukkansu sun nuna surar tsoffin gine-gine. A cikin yawancin shaguna da kantunan da ke gefunan 2 ake sayar da kayayyaki ko kuma magunguna, sa'an nan kuma, masu fasahar gargajiya su kan nuna wasannin kwaikwayonsu irin na musamman a titin. Madam Sha Xianping, wata jami'ar kwamitin harkokin titin Hefangjie ta gaya mana cewa,

'A titinmu, mu kan shirya wasu bukukuwa bisa lokuta daban daban na wata shekara. A lokacin bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, mu kan shirya bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin tun daga rana ta farko zuwa rana ta 15 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Muna nuna al'adun gargajiya da al'adun gargajiya da Sinawa suka saba bi. Ta haka masu yawon shakatawa ba kawai suna iya yawo a kan titinmu ba, har ma suna iya kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya na kasar Sin.'

Baya ga gine-gine masu halayen musamman, a titin Hefangjie, abinci iri daban daban suna iya kashe wa mutane ido, sai ire-iren abubuwan kalaci kawai ya wuce dari guda. Ban da wannan kuma, wakokin da masu sayar da abubuwan kalaci suka rera na da ban sha'awa ainun. Ga shi, wani mai kanti yana sayar da wainarsa.


1 2 3